Shugabannin ‘Yan Bindiga 7 a jihar Katsina Sun Yada Makamai, Suna Neman Sulhu da Gwamna Masari.
Shugabannin ƴan bindiga bakwai a jihar Katsina sun ajiye makamansu tare da neman gwamnatin jihar domin yin sasanci mai ɗorewa.
Mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar kan lamurran tsaro, Ibrahim Ahmad Katsina ya bayyana hakan ga gidan Talabijin na Channels a ranar Juma’a. Ya bayyana cewa shugabannin ƴan bindigan sun gano abin da gobe zata haifar musu don hakan suka tunkari gwamnatin jihar domin tabbatar da samun cigaba. Kamar yadda Ahmad Katsina ya bayyana, ƙoƙarin gwamnatin jihar kan ƴan jihar tuni ya fara kawo sakamako mai kyau ganin yadda farmakin ƴan bindiga ya ragu. Ya sakankance cewa duk wasu miyagun ayyuka da suka hada da ƴan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuka sun kusa zuwa ƙarshe sakamakon ƙoƙari na haɗin guiwa da aka samu tsakanin ƴan jihar da gwamnati wurin taimakawa jami’an tsaro. Hakazalika, ya tuna yadda gwamnatin jihar a baya-bayan nan ta horar da ƴan sa kai 1,100 waɗanda za su dinga taimakawa al’umma, kokarin da ya zama tamkar saƙo ga ƴan bindigan don su rungumi zaman lafiya.
Hadimin Gwamnan ya yi bayanin cewa gwamnatin jihar ta ƙaddamar da wani babban kwamiti ƙarƙashin jagorancin mataimakin Gwamnan jihar Mannir Yakubu, domin ɗauko ƙididdigar waɗanda rikicin ƴan bindigan ya ritsa da su. An yi hakan ne domin tabbatar da cewa ba a nuna halin ko in kula ga waɗanda lamarin ya shafa ba kuma don gujewa wani rikici bayan harin ƴan bindigan ya zo ƙarshe. “Muna amfani da sauƙaƙan dabarun sanin halayyar ɗan Adam ne wurin shawo kan abinda yara za su fahimta a wuraren da rikicin ƴan bindigan ya shafa. Wannan kuwa mun yi shi ne saboda gane cewa yaran da lamarin ya shafa za su so daukar fansa. Don haka ne mu ke tallafa musu. “Za mu samar da ayyukan yi ga matan da aka kashe mazansu, sana’o’i da kasuwanci kuma za mu kai ƴaƴansu makaranta. Wannan kokarin kuwa yana samar da abinda ake so.”
Magodara: Legit Hausa
Allah Ya mana maganin ƴan ta'adda
ReplyDelete