Gaskiyar abun da yake faruwa da Polaris bank
Me yake faruwa a Polaris Bank?
________________________________
Ina so mutane su yi haƙuri su karanta wannan rubutun zuwa ƙarshe.
Abin da yake faruwa a Polaris Bank, wato tsohon Bankin (Skye Bank) a gaskiya ba maganar posting da wata ma'aikaciyarsu ta yi ba ne farkon matsalar.
Babban Bankin Nigeria CBN ya dakatar da Bankin Skye Bank daga aiki a 2018, Kuma ya mallakawa Polaris Bank, wato a takaice Polaris Bank ta saye Skye Bank, wani abu me kama da na Access Bank da Diamond Bank.
~ Su waye suka mallaki Polaris Bank?
Kai tsaye wasu Musulmai ne masu kokari da kishi suka saye Skye Bank suka bude Polaris Bank bisa dokoki da tsarin CBN Dana wasu hukumomi a kasar nan.
~ Ana cikin haka sai suka yi kokarin shigo da wasu tsare tsare irin na Stanbic IBTC, Stabic Islamic Bank ne irin Ja'iz da Taj Bank, toh sai suka hadu da makirci daga sama can☝️ da Kuma kasa nan, an gane ai.
~ Toh sai aka shirya makirci domin a sayar da Lasisin Bankin, maganar taje har gaban shugaban kasa Buhari, kamar yadda kake gani a hoton jaridar Vanguard dake kasa👇 tun a watan August fa, ba yanzu ba.
~ Daga nan sai wata kungiya Mai suna HUWARI, tayi kira ga shugaban kasa Buhari kada ya bari a siyar da Bankin, maganar tayi nisa har taje gaban Majalisar Wakilai (Reps) kamar yadda kake gani a hoton dake kasa👇a cikin jaridar The Cable.
~ House of Representatives suka bayar da umarni kada gwamnatin Nigeria ta sayar da Bankin Polaris, aka ware mutane 20 daga Reps suje su duba wannan batun Kuma su kawo Bahasi (Report) wa National Assembly, saboda akwai makarkashiya a batun sayar da Bankin, domin Rahotanni sun bayyana Kadarorin da Bankin ya mallaka a fadin Nigeria sun Kai Naira Trillion daya da Biliyan dari biyu (1.2 Trillion Naira).
~ Amma aka ce a siyar dashi a Naira Biliyan 40🙆😳
~ Duk makircin da aka kulla sai Allah ya dinga warwarewa, daga karshe sai aka rasa yadda za ayi aka je aka nemi wata ma'aikaciyar su ta fitar da takarda a Boye daga Ofishin Manajan cewa Bankin bai yarda Ma'aikatan sa Musulmi su dinga fita sallah ba musamman a lokacin Juma'a.
~ Har taje ta saka a Social Media, nan da nan sai Sahara Reports suka dauki nauyin yada bayanin, da kururuta wannan takardar cewa daga Management din Bankin ne.
~ Sai Musulmin Nigeria suka fusata, suka ce sai sun karya Bankin sai sun kaishi kasa, saboda wannan batun sallar.
~ Makircin da aka kulla na karshe akan Bankin da yayi tasiri kenan guda daya, an hada Musulmi fada ko Kuma an saka musu tsana da kin Bankin.
~ Amma Bankin Mallakar waye? kaje Website din Polaris Bank wajen Board of Directors, zaka ga Wanda ya mallaki Bankin.
~ Gashi nan na saka hoton sunayen Board of Directors din, kaje ka duba da kanka, zaka ga Muhammad K. Ahmad shine jagora daga cikin wadanda suka mallaki Bankin, ko kace shine ma me Bankin.
~ Idan baka nutsu da haka ba kaje ka duba Wikipedia, zaka tabbatar da haka, duk gasu nan na saka a kasan posting din nan👇
Polaris Bank sun fito sun bayar da hakuri, sunce zasu dau mataki, Musulmi suyi hakuri Amma Ina babu Wanda ya yarda da maganar tasu, saboda su kadai suka San yakin dake tinkarar su.
~ Ni kaina da nake rubutun nan (Abdulhadi) Bankin Skye Bank (Polaris) shine Bankin dana fara budewa a rayuwa ta, a 2009.
~ Kuma har yanzu ban rufe ba, sai dai na manta Account number din.
Lokacin da naji labarin nace toh idan haka ne nima zan rufe Account dina, Amma bari nayi bincike tukun, wannan abinda bincikena ya fara ganowa kenan.
Still on the process of investigations......
~ So, idan Makiya sun bi ta fadar shugaban kasa basu yi nasara ba, sun bi ta Reps ba suyi nasara ba, toh sunyi nasara ta wajen mu saboda bamu bin labarai mun fi bin labaran da suka fi yawa ko basu da tushe.
Kuma har yanzu Ina kan Bincike akan wannan batun ban gama ba, iya abinda na fara ganowa kenan.
Allah yasa mu dace....
✍️
Abdul-Hadi Isah Ibrahim.
Comments
Post a Comment