Ƙarin bayani dangane da RENEC

 RENEC Update....

___________________________

Ana cigaba da shirye shiryen bude Trading na RENEC Coin na kamfanin Remitano wanda mutane Miliyan 1 da dubu dari biyu suka yi Mining, suka tara shi akan waya a tsawon watanni 16, gyara ko correction da muka samu game da supply din da za'a sake a ranar farko (Al-Hamis mai zuwa) sune Coins guda dubu dari 148,231 ba dubu dari biyar da muka bayyana da farko ba.

   ~ Dalili akan haka kuwa shine, idan ka Kalli Totel Supply na RENEC zaka ga 73,227,247 million ne, a cikin su akwai 35,575,446 na Miners.


  ~ Bisa yadda Remitano suka tsara babu wani Coin da za'a sake wa Public, purposely saboda mutane kawai bayan na Team dana wadanda suka yi Mining toh babu wani RENEC din da za'a bayar dashi a kasuwa.

   ~ To bisa wannan tsarin idan ka Kalli abinda za'a bayar wa Miners kowane Sati zaka ga Coins ne guda dubu dari 148,231 rak, ta Yaya muka gano haka?

  Ta hanyar buga yawan abinda Miners suke dashi 35,575,446 ÷ 5 = 7,115,009


   ~ Hakan yana nuna duk shekara Miners zasu samu Coin guda Miliyan 7 da Dubu 115.

  ~ Sai ka raba shi zuwa watannin 12, wato:

7,115,009 ÷ 12 = 592,924

Miners zasu samu RENEC dubu dari 592 duk wata, to sai ka sake raba shi into 4 weeks, sai kace:

             592,924 ÷ 4 = 148,231

Wato duk sati Miners zasu samu RENEC 148,231 kadai, haka za'a yi tayi har October 2023 in sha Allah. Daga nan Kuma za'a dinga sakewa duk karshen wata, Asabar din karshen wata, lissafin ba zai canza ba, releasing din ne kawai zai canza.


   ~ Toh sai dai Kuma idan muka Kalli lissafin yana nuna cewa ranar Al-Hamis za'a sake wa Miners nasu na farko, ba Asabar ba, idan an bayar ranar Al-Hamis toh za'a tsallake Asabar din da take biye da 20 ga October, sai anje Asabar 29 ga October din sai a cigaba.

   ~ Haka lissafin releasing din zai kasance, saboda babu wani Coin da aka ware wa Public buyers, wato Non Miners, idan ba'a bayar ba Kuma toh wannene public zasu samu? Babu!!!


  ~ Sai dai in Kuma zasu bayar da dama kowa ya saya Wanda aka bayar da Miners, su Miners sai a bar nasu ba zasu cire ko su siyar ba sai Asabar toh da hakan zai fi zama alkhairi, domin public buyers za suyi ta zuba kudi akan RENEC din da Miners zasu kwashe ranar Asabar ne, Wanda Ina zaton target din masu Remitano kenan.

   ~ Kudin da zasu bayarwa Miners ba daga wajen su kadai zai fito ba, zai fito ne daga kasuwa, abinda Remitano za suyi kawai shine providing Liquidity a karon farko.

Ba kowa zai fahimci wannan hikima da tsarin ba.


    ~ Toh wani zai ce ai Coin din da za'a sake zasu Fi dubu 148,000 saboda ai akwai na Team, wato Remitano Core Team, Team suna da 10 million RENEC (10,705,246), sai muce Eh haka ne Amma nasu an riga an bayyana abinda za ayi dasu guda biyu:

  ~ Na farko, Staking for 5 years.

  ~ Na biyu, Lock Up for 5 year.

Dan haka babu yadda za'a yi dasu, suna nan in circulation, Amma ba za'a iya yin komai dasu ba, Miners ne kawai zasu iya siyar da nasu.


   ~ Idan ka buga lissafi zaka ga cewa Team suna da 10,705,246 ka raba shi into 5, zai baka Miliyan 2,141,049 duk shekara za'a sake musu.

To ka buga shi into 12 Months, zai baka RENEC guda dubu 178,420.

Ka sake raba shi into 4 zai baka 44,605 duk sati zasu samu.

  ~ Idan ka hade abinda za'a sake wa Miners duk sati da abinda za'a sakewa Team gaba daya Coins guda dubu 192,836 ne rak, out of 73 million.

Ta Yaya za ayi wannan abun yayi araha Malam?


 ~ Kuma ana sake nasu na Team direct zai tafi zuwa ga Lock Up and Staking ne, ba kamar naka bane idan an baka, sai kaga dama kayi lock up ko staking.


  ~ Remitano sun kawo DPOs akan Blockchain din su, wato (Delegated Proof Of Stake) kaima idan an baka RENEC dinka zaka iya shigar dashi, daga nan RENEC dinka zasu dinga karuwa base on APR din da zasu bayyana nan gaba.

   ~ (Sai a kula, Staking ba Haramun bane a Musulunci, saboda may be wasu zasu iya cin karo da wani Posting da nayi a 2019 da 2020 Wanda nake cewa staking Haramun ne a Crypto, amma daga baya na sauka akan wannan saboda bincike da mukai akai, daga baya na bayyana dalilan rashin haramcin).


   ~ Abu na karshe shine maganar da wasu suke yi cewa wai ba iyaka 73 million bane supply din RENEC, wai ai sunce the total supply at the time of launch is 73 million, wai hakan yana nuna akwai wasu da za'a karo nan gaba, Wanda ba haka abun yake ba.

    ~ Wannan kuskuren fahimta ne, domin a Coin Matrix din an bayyana komai, idan akwai wasu da za'a Kara nan gaba toh a wajen Coin Matrix din zasu bayyana, may be wadanda suke fadin hakan basu Saba bin Coins da Tokens bane, babu yadda za ayi a raba Token ko Coins ba tare da an bayyana abinda ya rage a kasa ba.


   ~ A irin wannan tsarin shine Total supply yake nufin Maximum supply, idan ba a Irin wannan tsarin bane ake samun banbanci tsakanin Total supply da Maximum supply, da kuma Circulating Supply.


   ~ Abu na karshe, bisa ga wadannan bayanan kada kayi zaton farashin RENEC farashi ne da zaka iya kwasa ko saye shi da araha, bama son mu sakawa mutane dogon buri ko kwadayi, amma gaskiya RENEC ba zai fito da arahan da talaka zai sayi guda goma ko sama da haka ba.

   ~ Merchant Directory kawai idan kaje ka gani akan Remitano Kai kasan ba'a yi Coin din don kowa da kowa ba, anyi ne kawai don wadanda suke da kudi da wadanda suka yi mining luckily cikin hukuncin Ubangiji.

Domin ko a Dala 'daya yazo zai tsere wa mutane.


Sauran bayanan zasu zo gobe in sha Allah.

Allah yasa mu dace....

✍️

Abdul-Hadi Isah Ibrahim.



Comments

Popular posts from this blog

Gaskiyar abun da yake faruwa da Polaris bank

Gwamnatin Najeriya ta nemi afuwar ɗalibai da iyaye kan yajin aikin ASUU